✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta ba mutanen da ambaliya ta shafa a Najeriya Dala miliyan daya

Ambaliyar ruwa ta janyo illa ga kusan mutum miliyan 2.8 a fadin kasar.

Gwamnatin Amurka za ta bayar da tallafin da ya kai na dala miliyan 1 ga mutanen da ambaliya ta yi wa barna a Najeriya.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurkar ya fitar a Abuja a ranar Alhamis.

Tallafin da za ta bayar ta hanyar hukumarta ta raya kasashe masu tasowa (USAID), zai kasance na gaggawa.

Jakadiyar Amurkar a Najeriya, Mary Beth Leonard, ta ce suna cike da jimami kan wadanda ambaliyar ta shafa da suka rasa abubuwa da dama – hanyoyin rayuwarsu da gidajensu har ma da ’yan uwansu.

BBC ya ruwaito Mary Beth tana cewa, Amurka za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.

Sannan za ta yi aiki tare da hukumomin kasar yayin da ake sa ran samun karin ruwan sama da ambaliya a watan Nuwamba, a wasu sassan kasar saboda sauyin yanayi da rashin magudanun ruwa, da nufin samar da karin taimako idan akwai bukatar haka.

Amurkar ta kuma ce ta damu da yiwuwar ruwan ambaliyar da ya taru a wurare zai iya kara hadarin kamuwa da cutar amai da gudawa da sauran cututtuka da ake dauka a ruwa, a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

A wadannan jihohin an samu barkewar cutar kwalara a watan Agusta da Satumba, kuma ta kama mutum akalla 7,750 in ji sanarwar.

Ruwan sama mai tsanani da ya haddasa ambaliya ya janyo illa ga kusan mutum miliyan 2.8 a fadin kasar.

Gidaje da dama sun lalace ko ma sun rushe a sanadiyyar matsalar wadda ta tashi miliyoyin mutane daga gidajensu.

A wannan shekarar da ake ciki an samu rahotannin bullar cutar ta amai da gudawa a jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriyar.