✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta ba Ukraine makamai masu linzami don kare kanta daga Rasha

Wata majiya ce ta tabbatar wa da AFP haka

Amurka na shirin aika wa kasar Ukraine makamai masu linzami don ta yi amfani da su wajen kare kanta daga hare-haren da Rasha ke kai mata.

Wata majiya mai tushe ce ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP hakan ranar Litinin.

Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunata ta ce, “Shugaban Amurka Joe Biden ya sayi kayayyakin samar da tsaron sama don nuna fifiko ga kasar Ukraine . 

“Akwai yiwuwar fitar da sanarwa a satin nan da muke ciki, na siyan makaman kariya masu linzami, kuma masu matsakaici ko nisan zango daga kasa zuwa sama, da ma sauran muggan makamai domin tallafawa kasar Ukraine ta samu galaba kan Rasha a yakin da suke gabzawa.”, inji majiyar.