✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka za ta horar da sojojin Ukraine fasahar harbo makamai masu linzami

Sojojin za su tafi Amurka ne a mako mai kamawa

Akalla sojojin Ukraine 100 ne za su tafi Amurka a farkon mako mai kamawa don samun horo kan fasahar kakkabo makamai masu linzami.

Hakan dai wani yunkuri ne na kara samun kariya daga luguden wutar da Rasha ke yi a kan Ukraine din.

Ukraine dai ta bukaci Amurka da ta samar mata da na’urorin kakkabo makaman, domin ta rika amfani da su wajen harbo jirage da kuma makamai masu linzamin da Rasha ke harba mata.

A yayin ziyarar da ya kai Amurka a watan Disambar bara, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy ya ce makaman za su taka muhimmiyar rawa wajen dakile hare-haren mamayar Rasha a kansu.

Wannan ne dai karon farko da Ukraine za ta kwashe sojojinta daga bakin daga zuwa Amurka don su karbi horo, kodayake a baya ta sha tura su kasashen Turai domin samun horon a kan wasu abubuwan da ma suka fi wannan sarkakiya.

Galibi dai a kan kwashe tsawon lokaci kafin kammala samun horo a kan fasahar, amma Ukraine ta ce za a takaita shi don su samu su koma bakin daga a kan kari.

Da zarar sun kammala samun horon kuma, makaman da dakarun za su samu, kari a kan na Amurka da NATO, za su taimaka wajen yakin da kasar ta shafe wata 11 tana fafatawa da Rasha.