✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta taimaka wa Najeriya magance matsalolin yanayi

Amurka ta yi wa Najeriya alkawarin taimako domin kowama amfani da makamashin iskar haidurojin

Gwamnatin Amurka ta yi alkawarin tallafa wa Najeriya wajne magance matsalar sauyin yanayi da ta muhalli da take fama da su.

Wakilin Shugaban Amurka na Musamman, Mista John Kerry ne ya bayyana hakan, a wani zauren tattaunawa da manema labarai ranar Talata a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya.

Kerry ya kuma yaba wa Shugaba Buhari, bisa kokarinsa na samar da shirye-shirye da ayyuka na musamman da za su rage matsalolin yanayi da muhalli a Najeriya.

“Babban cigaba ne shugaban ya samar a Najeriya kan sauyin yanayi, kuma na ji dadin yadda na ga shirye-shiryen da gwamnatinsa ke yi domin kawo karshen matsalar.

“Lallai za mu zuba makudan kudade a wadannen shirye-shiryen, domin ganin an magance matsalar baki daya.

“Wani alkawarin kuma shi ne za mu duba yiwuwar komawa amfani da makamshin iskar haidurojin domin kammalar abubuwan cikin sauri a cikin kasar,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Idan aka cim-ma hakan, ba Najeriya kadai ba, duk duniya ma za ta amfana.”

Kerry ya ce dimbin albarkatun man fetur da iskar gas da kasar ke da su ne ya taimaka wajen jefa ta a matsalar yanayin da muhalli.

Amma ya ce, “Za mu ci gaba da tunanin yadda za mu yi aiki tare da gwamnatin Najeriya da ma kamfanoni masu zaman kansu, domin tabbatar da mun cim-ma manufarmu nan da shekarar 2050.”