✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ayyana makokin kwanaki 2 bayan kashe mutum 41 a Burkina Faso

Harin na baya bayan nan dai shi ne mafi muni a Burkina Faso.

Gwamnatin Burkina Faso ta ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki biyu tun daga Lahadin nan, bayan da gungun ’yan ta’adda masu ikirarin Jihadi suka kashe mutane akalla 41, a wani hari da suka kai lardin Loroum da ke Arewacin kasar mai fama da rikici.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar da yammacin ranar Asabar din da ta gabata ta bakin wani mai magana da yawunta, Alkassoum Maiga, ta ce tawagar masu binciken da ta tura ne suka gano gawarwakin mutanen 41 da ’yan ta’addan suka yi wa kwanton bauna.

Gwamnati ta ce wadanda suka mutun sun hada da jami’an rundunar jami’an tsaron sa kai, wadanda aka fi sani da dakarun VDP, wadanda aka kafa domin tallafawa sojojin Burkina Faso wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwaito jami’an tsaron sa-kai na VDP dai na samun horon tsawon kwanaki 14 ne kafin tura su aikin sinitiri dauke da kananan makamai a yankunan, Burkina Faso masu fama da matsalar tsaro.

Sanarwar gwamnati ta ce daga cikin wadanda harin na ranar Alhamis ya rutsa da su har da Ladji Yoro, jagoran masu tsaron sa-kai na VDP, inda ta kara da cewar, har yanzu ana ci gaba da tantance wadanda lamarin ya shafa.

Bayanai dai sun ce, ’yan ta’adda sun yi wa ’yan sa kan kwanton Bauna ne, a lokacin da suke yi wa wani ayarin ‘yan kasuwa rakiya a kusa da Ouahigouya, wani gari da ba shi da nisa da kan iyakar Mali.

Harin na baya bayan nan dai shi ne mafi muni a Burkina Faso, tun tsakiyar watan Nuwamba inda aka kashe mutane 57 da suka hada da Jandarmomi 53.

Kamar makwabtanta da suka hada da Mali da Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso na fama da tashe-tashen hankula tun shekara ta 2015, sakamakon kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi, wadanda suka yi wa kungiyar Al-Qaeda da IS mubaya’a.

Hare-haren mayakan dai ya yi sanadin mutuwar mutane akalla dubu 2,000 tare da raba wasu miliyan 1.4 da muhallansu a kasar ta Burkina Faso.