✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba da hutun Sabuwar Shekarar Musulunci a Sakkwato

Tambuwal ya ayyana ranar Litinin ta zama ranar hutun Sabuwar Shekarar Musulunci.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana ranar Litinin ta zama ranar hutu domin shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci.

Gwamna Tambuwal ya ce bayan tattaunawa da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, kan shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci a wannan Jumu’ar, “Na ayyana Litinin 1 ga watan Agusta 2022 ta zama ranar hutu ga ma’aikatan gwamnati a fadin Jihar Sakkwato.”

Tambuwal ya roki mutane su yi amfani da lokacin hutun wajen nuna kyawawan dabi’u, kamar bayar da sadaka da yin addu’o’in zaman lafiya da samun shugabanci na gari.

“Mu ci gaba da bin karantarwar addini a wannan watan ganin yana cikin watanni hudu da ke da daraja, da aka haramta zubar da jini da wasu manyan laifuka.

“Allah Ya sada mu da rahamarSa da gafara, ina fatar samun dacewa a shekarar Musulunci,” a cewar Tambuwal.