✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba hamata iska kan Dokar Man Fetur a Majalisar Tarayya

Al'ummomi masu arzikin mai sun dambace a zaman sauraron ra'ayoyi kan Dokar Mai Fetur (PIDB)

Wasu al’ummomi masu arzikin albarkatun man fetur sun ba wa hamata iska yayin zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan sabuwar dokar bunkasa bangaren man fetur (PIDB) a Majalisar Wakilai.

A yi ta kai wa juna naushi ne a fadan da ya kaure, bayan Kwamitin Majalisar Wakilai ya gayyato al’umma ta farko da za ta gabatar da bayanan da take tafe da shi.

A zaman na ranar Alhamis, Kwamitin Majalisar ya ce sauran al’ummomin za su biyo baya da zarar an kammala sauraron na farkon.

Sai dai hakan bai yi wa wasu al’ummomin dadi, inda suka ce allambaram suka fara yi wa juna ihu, har ya kai ga cacar bakin ya koma dambe.