✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba iyalan ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki a Zamfara N5.1m

Kwamishinan ya ce tallafin zai dada zaburar da sauran jami’an da suke aiki.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara ta bayar da Naira miliyan biyar da dubu dari daya a matsayin inshora da kuma tallafin Babban Sufeton ’Yan Sanda ga iyalan jami’anta biyar da suka rasu a bakin aiki.

Da yake gabatar da cakin kudin ga iyalan mamatan, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ayuba Elkanah, ya ce an mika musu tallafin ne domin su rage radadin rayuwar rashin ’yan uwan nasu.

Kwamishinan ya ce tallafin ya zo ne a lokacin da aka fi bukatarsa, kuma zai dada zaburar da sauran jami’an da suke aiki.

A cewarsa, Babban Sufeton ’Yan Sanda, Usman Alkali Baba, ya damu matuka da walwalar jami’ansa, musamman a bangaren biyan inshorar rayuwa da sauran hakkokin wadanda suka mutu a bakin aiki.

Daga nan sai ya shawarci iyalan mamatan da su yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace, yana mai cewa rundunar a Jihar ta gabatar da makamancin wannan tallafin ga iyalan jami’anta da dama da suka rasu a baya.

Daya daga cikin iyalan mamatan, Usman Musa, wanda ya karbi Naira miliyan uku da dubu dari da sittin, a madadin dan uwansa, ASP Dankane S Rafi, ya mika godiyarsa ga Babban Sufeton.