✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba Ma’aikatan Zamfara hutun mako daya saboda rajistar zabe

INEC ta saka ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar karshe da za a rufe aikin rajistar katin zabe.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bai wa ma’aikatan jihar hutun mako daya domin su yi rajistar katin zabe da ake gudanarwa yanzu haka a fadin kasar.

Kwamishinan Yada Labarai na Zamfara Ibrahim Dosara ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar.

Sanarwar ta ce Gwamna Bello Matawalle ya amince da ba da hutun ne daga Litinin, 20 zuwa 24 ga watan Yuni.

“A sakamakon wannan sanarwa, an umarci dukkan Kwamishinoni da masu bai wa gwamna shawara da Sakatarori da sauran ma’aikatan gwamnati da jami’an jam’iyyun siyasa da su saka ido kan yadda aikin rajistar ke tafiya,” a cewar kwamashinan.

Bayanai sun ce kungiyoyi da ’yan gwagwarmaya a Najeriya na ci gaba da kira ga Hukumar Zabe ta kasa INEC da ta tsawaita wa’adin yin rajistar, suna masu cewa mutane da dama ba su samu damar yi ba saboda karancin kayan aiki da kuma cunkoso.

Tuni dai INEC ta saka ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar karshe da za a rufe aikin rajistar.