✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ba wa Abale kyautar dalleliyar mota

Dan Kwairon Tafa ya ba Daddy Hikima kyautar mota bayan wadda Rarara ya ba shi.

Alhaji Dan Kwairon Tafa ya ba Daddy Hikima wanda aka fi sani da Abale ko Ojo kyautar dalleliyar mota.

Mashiryin shirin ‘A duniya’, Tijjani Asase ne ya bayyana hakan, inda ya sanya hoton motar sannan ya ce, “Allah Ya hada mu da masoyanmu.

“Muna godiya da kyautar mota da Dan Kwairon Tafa ya ba Daddy Hikima wato Abale. Mun gode wa Allah; Allah Ya saka da alherinSa.”

Abale ya yada labarin, sannan ya ce, “Allah Ya taimaki maigida. Allah Ya jikan magabata.”

A kwanakin Aminiya ta ruwaito cewa fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya ba wa Abale kyautar mota kirar Honda samfurin ‘Discussion continue’, kyautar da Daddy Hikima ya bayyana cewa ba zai taba mantawa da ita ba kasancewar kafin nan, babur yake hawa domin zirga-zirga.

Abale ya Dade yana fafutika a masana’antar Kannywood, inda ya kasance yana aikin cigaban shiri.

Aminiya ta ruwaito Abale nas ne, sannan ya kasance yana taimakawa wajen sayar da tikiti a sinimar Ado Bayero idan ana haska fim.

Daga ya samu daukaka bayan fitowarsa a matsayin dan daba a fim din na ‘A Duniya’, daga nan kuma ya fara fitowa a fina-finai da dama.

Kodayake ya fito a wasu fina-finan a matsayin dan daba kafin ‘A duniya’ irinsu ‘Haram’ da sauransu.

Daddy Hikima, an yi manyan masu fitowa a matsayin ’yan daba a Kannywood, irinsu Shuaibu Lawal Kumurci da Tijjani Asase da Isa West da sauransu.

Sai dai Abale ya shiga fagen da kafar dama, inda a yanzu yake jan zarensa a masana’antar baki daya, ba ma a matsayin dan daba ba.