✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba wasu makarantu izinin yin jarabawa a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin gudanar da jarabawar zangon karatu na uku ga makarantu da ke amfani da manhajar karatu ta kasashen waje. Karamin…

Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin gudanar da jarabawar zangon karatu na uku ga makarantu da ke amfani da manhajar karatu ta kasashen waje.

Karamin Ministan Lafiya, Chukwumeka Nwajiuba ya sanar da haka a taron hadin gwiwa na Kwamitin Kar-ta-kwana na Fadar Shugaban Kasa kan Yaki da COVID-19.

“Tabbas makarantu da ke amfani da manhajar karatun kasashe waje a Najeriya da ke neman gwada yin jarabawarsu ta zango na uku za su iya”, inji shi.

Ya ce makarantu masu zaman kansu da ke da izinin amfani da manhajar karatun kasashen waje, an yi su ne domin ‘ya’yan baki da jakadu, ta yadda idan ‘ya’yansu suka koma kasashensu za su iya ci gaba da karatu a duk sadda bukatar hakan ta taso.

“Idan har makarantun za su iya yin karatu ta intanet bisa manhajar da suke bi, kuma sun zabi yin hakan domin kammala darussa, to an sahale musu hakan. Ba mu ce kada a ci gaba neman ilimi ba,” inji ministan.

Sharuddan bude makarantaun cikin gida 

Gwamnatin Tarayya ta kuma gindaya sharudda da suka wajaba a  kan makarantu a dukkan matakai a Najeriya kafin a sake bude su.

A ranar 19 ga watan Maris, 2020 gwamnatin ta rufe dukkan makarantu a kokarinta na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Karamin Ministan Lafiya Chukwuemeka Nwajiuba ya ce kafin a sake bude makarantu dole ne kowace makaranta ta samar da wadannan abubuwa:

  1. Samar da kayayyakin wanke hannu.
  2. Auna zafin jiki.
  3. Kashe kwayoyin cuta a daukacin jiki a dukkannin kofofin shiga azuzuwa, ofisoshi, dakunan kwanan dalibai da sauransu.
  4. Kashe kwayoyin cuta a ko ina a fadin makarantar.
  5. A yi iya kokari wurin tabbatar da kula da kuma kare lafiya.
  6. Tabbatar da bayar da kariya a azuzuwa da ofisoshi da zauran wurare.

Duk da haka Ministan ya gargadi makarantu da su guji budewa ba tare da samun izinin yin hakan daga Gwamnatin Tarayya ba.

“Yayin da muke kokarin sassauta dokar kulle da zai kai ga bude makarantu, ina kira ga dukkan shugabannin makarantu kada su jira sai an sanar da sake bude makarantu kafin su ce za su dauki matakan da suka dace na bin ka’idodi da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta shimfida.”

A ranar Talata ne Aminiya ta ruwaito yadda jam’ian hukumar NCDC suka hana dalibai komawa makaranta a jihar Kuros Riba.

A makon jiya ne Gwamna Ben Ayade ya bukaci a bude makarantu uku a mazabun ‘yan majalisar tarayya uku da ke jihar a matsayin gwaji.

Jihar Kuros Riba ita ce kadai kawo yanzu ba a samu bullar cutar coronavirus ba fadin Najeriya.