✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An bai wa Zulum lambar yabo a Jami’ar Ibadan

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya lashe kyautar lambar yabo ta tsofaffin daliban Jami’ar Ibadan da ke Kudancin Najeriya. Gwamna Zulum ya samu kyautar…

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya lashe kyautar lambar yabo ta tsofaffin daliban Jami’ar Ibadan da ke Kudancin Najeriya.

Gwamna Zulum ya samu kyautar tsohon dalibi na shekarar 2020, wanda shi ne na biyar da ya taba lashe wannan kyauta tun 1973.

Aminiya ta ruwaito cewa, kungiyar tsofaffin daliban jami’ar ce ta yanke hukuncin bayar da lambar yabon bayan tuntubar ’ya’yanta da ke fadin duniya.

Zulum wanda Farfesa ne a Ilimin Kasa da Ruwa, ya yi jami’ar ne tsakanin shekarar 1997 zuwa 1988 inda ya samu shaidar digiri na biyu a kimiyyar noma gabanin komawarsa jami’ar Maiduguri inda ya yi digirin-digirgir a 2009.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka yi bikin karrama gwamnan a dakin taro na Dame Edith Okowa da ke Jami’ar, wanda ya samu halarcin Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq da kuma takwaransa na Jihar Osun, Gboyega Oyetola.

Tsohon shugaban kungiyar tsofaffin daliban wanda ya mika wa Zulum lambar yabon, Dokta Kemi Anthony, ya ce an yi la’akari ne da yadda Zulum ya zama zakaran gwajin dafi a kokarin da yake yi na jagorantar Jihar Borno.

Haka kuma Emina ya ce, Gwamna Zulum ya cancanci wannan lambar yabo kasancewar yadda ya zama abin misali a fagen kwazo a ciki da wajen Najeriya.

A jawabinsa, Zulum ya ce ya dauki wannan kyauta a matsayin kalubalen da zai kara masa hazaka da jajircewa wajen riko da akalar jagoranci da ta rataya a wuyansa.

“Ina ganin wannan kyauta a matsayin kalubale, saboda haka ina mai tabbatar da wannan taron cewa babu wani abu da wannan kyautar za ta kara mani sai karfin gwiwa da hazaka doriya a kan wacce nake yi a yanzu,” in ji Zulum.

Gwamnan ya kuma yaba wa dukkanin malaman da suka koyar da shi yayin kasancewarsa dalibin Jami’ar a tsakanin shekarar 1997 zuwa 1998.

Daga cikin wadanda suka yi rakiyar Zulum zuwa taron akwai tsohon Gwamnan Borno, Kashim Shettima, Sanata Muhammad Ali Ndume, Sanata Abubakar Kyari da wasu kusoshin gwamnati na Jihar Borno.

Daga shekarar 2019 kawo yanzu, Zulum ya lashe kyaututtuka na Gwamna mafi kwazo daga gidajen jaridu da daban daban a fadin kasar.