✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An bankado almundahanar N8.5bn a Majalisar Dokoki ta Kasa

Badakalar Naira biliyan 5.5 a Majalisar Wakilai da kuma Naira biliyan uku a Majalisar Dattawa da

Ofishin Mai Binciken Kudi na Tarayya ya gano badakalar Naira biliyan 8.5 a zaurukan Majalisar Dokoki ta Tarayya.

Rahoton binciken kudin ya gano yadda shugabancin zurukan biyu suka kashe Naira biliyan uku a Majalisar Dattawa da wasu biliyan 5.5 a a Majalisar Wakilai a shekarar 2019 ba tare da shaidar kashe kudaden ba.

Mai Binciken Kudi na Tarayya, Aghughu Adolphus, a rahoton, ya bankado yadda Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Hukumar Kula da Harkokin Majalisar Dokoki Ta Kasa suka kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.

Rahoton da ya gabatar wa Akawun Majalisar a watan Agusta ya ce  an kashe kudaden ne a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018 ba tare da cike takardun da suka dace ko rasidin kayan da aka saya ba.

An shekarar da ta gabata ne Kwamitin Kudaden Gwamnati na Majalisar ya kaddamar da bincike kan hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya daga 2015 zuwa 2018.

A watan Yunin bana ne kwamitin da rahoton binciken wata shidan da ya gudanar a kan hukumomin.

Da yake bayani kan lamarin, Shugaban Cibiyar Bin Diddigi da Tabbatar da Gaskiya a Harkokin Majalisa (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani, ya ce wannan abin takaici ne.

Sai dai a martaninsa, Akawun Majalisar Tarayya, Austen Adesoro, ya ce abubuwan da ake batu sun shafi shekarar 2019 kuma tun an shawo kansu.