✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bindige dillalan makamai 6 a Filato

Wani hafsan dan sanda da dan banga sun kwanta dama a musayar wutar.

’Yan sanda sun bindige dillalan makamai shida har lahira a wata musayar wuta a kauyen Kwoi da ke Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.

Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel Ogaba, ya ce an yi jami’ansu sun yi artabun ne a ranar Litinin bayan Rundunar ta samu rahoton ayyukan masu fasakwaurin makaman a yankin.

“Sai aka tura Rundunar Tattara Bayanai da kai dauki karkshin Ofishin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, da kuma jami’an da ke Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Mangu, da Rundunar hadin gwiwa ta STF da ’yan banga zuwa wurin.

“Bata-garin na ganin jami’an tsaron suka bude musu wuta amma saboda kwarewar jami’an tsaron da kuma karfin makamansu, suka bindige mutum daga cikin bata-garin, sauran kuma suka ranta a na kare da raunukan harbi.

“Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda uku.

“Sai dai kuma wani Sufeton Dan Sanda da mai suan Abdulrahaman Isah wanda shi ne Kwamandan Rundunar Tara Bayanan da ke Mangu da wani dan banga mai suna Hassan Mohammed sun kwanta dama,” inji shi.

ASP Ubah ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo wadanda suka tseren domin su girbin abin da suka shuka.