Daily Trust Aminiya - An bindige mutum 11 a Binuwai

’Yan bindiga

An bindige mutum 11 a Binuwai

Akalla mutum 11 sun rasu a hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Jihar Binuwai.

Maharan sun bindige mutum shida tare da yin awon gaba da wasu mata a kauyen Anyom na Karamar Hukumar Katsina-Ala bayan sun yi kutse a gonaki.

Sakataren Yada Labaran Karamar Hukumar, Tertsea Banga, ya “tabbatar da mutuwar mutum shida, wasu da dama kuma ba a san inda suke ba.”

Ya ce maharan da shanunsu sun kutsa ne cikin gonakin mutanen, suka kashe su tare da yin awon gaba da wasu mata.

’Yan bindiga sun kuma hallaka mutum biyar tare da jikkata wasu da dama a kauyen Zongo-Akiki da ke kusa da birikin soji a Karamar Hukumar Makurdi, wasu mutum biyar kuma sun bace.

Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, DSP Catherine Anene, ta ce tana kokarin tattara bayanai game da hakikanin lamarin.

Karin Labarai