✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An bude cibiyar bayar da fasfo cikin gaggawa a Abuja

An bude cibiyar din saukaka abubuwa ga hukumar da masu hulda da ita.

Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS), ta bude wata cibiyar samur da takardar Fasfo cikin gaggawa a Abuja.

Masu bukatar fasfo cikin kwana uku za su rika biyan N20,000, masu bukata nan take kuma N30,000, kamar yadda hukumar ta sanar.

Kakakin Hukumar, Sunday James, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “An fito da tsarin ne don saukakawa masu bukatar gaggawa.

“An bude cibiyar ce domin kara inganta ayyukan hukumar shige da fice da kasa.”

Ya kara da cewa hakan zai kara saukaka yadda al’amura suke a baya tare da rage cunkoso don kauce wa bazuwar cutar COVID-19.

Kwanturola Janar na Hukumar, Muhammed Babandede, ya ce matakin zai warware duk wata damuwa da ke tattare da samun fasfo a Najeriya.

“Cibiyar za ta taimaki wadanda za su biya kudin da aka ware, sannan za a ke samun sauki wajen mallakar fasfo,” a cewarsa.

Babandede, ya gargadi jama’a da su tabbatar sun biya kudadensu ta shafin hukumar na intanet, ko kuma bankunan da hukumar ta ware, don guje wa fadawa hannun ’yan damfara.