✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude filin jirgin sama na Abuja

A ranar Asabar 27 ga watan Yuni aka sake bude filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. An bude filin…

A ranar Asabar 27 ga watan Yuni aka sake bude filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

An bude filin jirgin ne a kokarin ci gaba da ayyukan sufurin jiragen sama a Najeriya, bayan rufe tashoshin jirgin sama a daukacin kasar watanni uku da suka gabata sakamakon bullar cutar COVID-19.

Rahotanni sun ce an dauki matakan kare yaduwar cutar a filin jiragin na Abuja da na Legas ta hanyar sanya alamun ba da tazara a wuraren da jama’a ke bin layi da ilahirin kujerun zama a harabar tashoshin da kuma kujerun cikin jiragen sama.

Kanfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ce an tanadi kayayyakin kariyar COVID-19 a tashoshin jirgin saman  da suka hada da na’urori da sinadaren wanke hannu.

An kuma zana alamomin ba da tazara, baya ga na’urorin gwada dumin jiki da manyan injina guda biyu da za su rika aikin tantance fasinjoji da aka tanadar.

Rahoton ya ce an kwashi ‘yan jaridan da ke ba da rahoton ayyukan Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) daga tashar jirgin sama ta Murtala Muhammad da ke Legas zuwa tashar jirgin saman Abuja a matsayin gwaji, inda suka shaida matakan kariyar da aka tsara a tashoshin.

A ‘yan makwanin da suka shude, Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeiriya ( NCCA) ta sanar da shirin bude tashoshin jirgin sama domin ci gaba da harkokinsu bayan an rufe su a wani mataki na kare yaduwar cutar.