✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude layukan waya a Katsina

An bude layukan sadarwa bayan wata uku da daukar matakin da nufin dakile ’yan bindiga.

Bayan wata uku da rufe layukan wayar salula a kananan hukumomi 17 da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi gami da rufe wasu kasuwannin dabbobi, ta bayar da umarnin bude su a ranar Alhamis.

Sanarwar bude layukan sadarwar ta fito ne daga bakin Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari a kan Harkokin Tsaro, Ibrahim Muhammad Katsina.

Ya ce gwamnatin ta yanke wannan shawara ne bayan lura da ta yi cewa an samu saukin ayyukan ta’addanci a jihar da kuma hidimar masu ba wa ’yan ta’addan wasu bayanai.

A cewarsa, da ma gwamnatin ta rafe layukan sadarwa ne a matsayin matakin wucin gadi da nufin dakile ayyukan ta’addanci da masu taimaka wa ’yan ta’adda a fadin jihar, musamman a tsakanin wadannan hukumomin 17 da ‘yan bindigar dajin da ake zargin barayin shanu da yin garuwa da mutane tare da kisan ba gaira ke kaiwa ke cin karensu babu babbaka.

Sai dai hadimin na Gwamna Masari ya kara yin kira ga jama’a da su ci gaba da ba gwamnati goyon baya domin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a fadin jihar da kasa baki daya.