✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude makarantar horar da ma’aikatan Hajji da Umara a Najeriya

NAHCON ta ce bude makarantar a zai inganta ayyukan hukumar a lokutan Hajji da Umara, da kuma cim-ma burinta na zama abar koyi a duniya.

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce samar da makarantar horas da ma’aikatanta kan aikin Hajji da Umara, zai sanya Najeriya shiga sahun kasashen da suka ci gaba a fasahar zamani.

Shugaban NAHCON, Zikrullah Hassan ya shaida wa taron bude makarantar a Abuja cewa hakan zai inganta ayyukan hukumar a lokutan Hajji da Umara, da kuma cim-ma burinta na zama abar koyi a duniya.

“Ina da yakinin makarantar za ta bada gudummawa wajen tabbatar da Najeriya ta zamo kasar da ke gaba-gaba wajen gudanar da inganccen aiki a lokutan Hajji da Umara.

“Haka kuma duniya ta ga ci gaba a fannin fasahar zamani ta kowanne bangare, don haka dole mu ma mu yi koya da haka”, in ji shi.

Ya kuma ce makarantar za ta samar wa da ma’aikatan sana’o’in dogaro da kai don cigaban su.