✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude makarantu a Kaduna

Dailbai za su rika zuwa makaranta da kayan gida.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da izinin bude makarantu a jihar daga ranar Laraba, 18 ga August, 2021, amma dalibai za su rika zuwa da kayan gida.

Daliban da gwamnatin ta amince su koma makaranta su ne ’yan aji uku a karamar sakandare da suke shirin rubuta jarrabawar kammala karamar sakandare.

Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar ta tsawaita hutun makarantu n firamare da sakandare a fadin jihar saboda yaki da sojoji ke yi da ’yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma.

Amma Sanarwar da Kwamishinan Ilimin Jihar Kaduna, Shehu Usman  Muhammad ya fitar a ranar Laraba ta ce, “Gwamnatin ta amince daliban JSS III da za su rubuta jabarrawar NECO BECE ranar 23 ga Agusta zuwa 6 ga Satumba,  2021 su kuma makaranta.

“Ana kuma umartar makarantun sakandare da su fara yi wa ’yan JSS III darussa daga 18 ga Agusta, 2021, sannan su sanar da daliban cewa da kayan gida za su rika zuwa makaranta,” inji shi.