✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude tashar cajin motoci masu amfani da lantarki a Sakkwato

A ranar Alhamis ne aka kaddamar da tashar cajin motoci masu amfani da lantarki irinta ta farko a tarihin Najeriya. Hukumar zayyana da tsara motoci…

A ranar Alhamis ne aka kaddamar da tashar cajin motoci masu amfani da lantarki irinta ta farko a tarihin Najeriya.

Hukumar zayyana da tsara motoci ta Najeriya, NADDC ce ta kaddamar da tashar a Jihar Sakkwato.

Shugaban Hukumar, Jelani Aliyu ne ya jagoranci kaddamar da tashar mai amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki a jami’ar Usman Danfodiyo da ke birnin Shehu.

Jelani ya shaida wa BBC Hausa cewa a yanzu duniya ta ci gaba, inda kusan ko ina ana amfani da motoci masu amfani da lantarki domin musanya su da masu amfani da man fetur.

Na’urar da ke tatsar hasken rana ta zama wutar lantarki a tashar
Jelani Aliyu yayin kaddamar da tashar a Sakkwato
Harabar tashar cajin motoci masu amfani da lantarki da aka kaddamar

“To kamar yadda muka sani, duniya yanzu ta karkata wajen amfani da motoci masu da lantarki, domin zamanin da ke amfanin da motoci masu amfani da man fetur da gas yana neman zama tarihi.”

“Shi ya sa muka ga cewa mu Najeriya ba a barmu a baya ba, muka tashi tsaye don ganin cewa mun taimaka wa irin wadannan kamfanonin a rika yin irin wannan motocin a nan Najeriya,” a cewar Jelani.

Idan ba a manta ba, a watan Fabrairun da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya a karon farko ta kaddamar da motoci masu amfani da wutar lantarki a maimakon man fetur.

Wannan ci gaba da Najeriya ta samu ya sanya ta cikin jerin kasashen da suka rungumi sabuwar fasahar amfani da motocin lantarki karkashin kamfanin kera motoci na Hyundai Kona da Stallion Group da ke Jihar Legas.