✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci gwamnatin Kano ta mayar wa da Jami’ar Maitama Sule kadarorinta

A halin yanzu dabi'ar kwacewa da sayar da kadarorin gwamnati a Jihar Kano ba sabon labari ba ne.

Kungiyar Malama Jami’o’in Najeriya (ASUU), ta bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta mayar wa da Jami’ar Yusuf Mataima Sule (YUMSUK) da ke jihar wasu fulotai da kadarori da ta kwace ta cefanar.

ASUU tana zargin gwamnatin Jihar Kano da kwacewa tare da cefanar da gine-gine Jami’ar da ke Kwanar Dawaki da kuma na Cibiyar Koyar da Sana’o’i duk a Karamar Hukumar Dawakin Tofa.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban ASUU reshen Jami’ar YUMSUK, Abdulrazak Ibrahim, ya bayyana lamarin kwace filayen jami’ar da ke babbar harabar makarantar a unguwar Tudun Yola a matsayin haramtacce.
A cewarsa, wannan kwacen filayen jami’ar da cefanar da su da gwamnatin Jihar Kano ke yi ba wani abu ba ne face dakile ci gaba da haifar da koma baya a harkokin ilimi, inda kuma ya gargadi gwamnatin da ta dakata haka domin samun zaman lafiya.
Ya ce “a halin yanzu dabi’ar kwacewa da sayar da kadarorin gwamnati a Jihar Kano ba sabon labari ba ne domin kuwa ya zama ruwa dare.
“Abin da ya fi ci mana tuwo a kwarya shi ne yadda gwamnatin ke kwacewa tare da sayar da kadarorin jami’ar da har yanzu kusan sabuwa ce da take da burin habaka.
“Gwamnatin ta kwace wani muhimmin gini a Kwanar Dawaki wanda nan ne yake zaman sashen nazari da gudanar da harkokin kiwon lafiya.
“A yanzu masu karatu a wannan sashe ba su da wani zabi da ya wuce su kukuta wani dan karamin gini a babbar harabar jami’a karin a kan wahalar da suke sha ta kai-komo wajen shiga lacca da daukar horo na gani da ido.
“A kwanan nan gwamnatin ta kwace mana wani gini da ke zaman Cibiyar Koyar da Sana’o’i a Karamar Hukumar Dawakin Tofa.
Wasu rahotanni sun ce ASUU ta yi barazanar gurfanar da gwamnatin Kano a gaban Kuliya idan har ba ta dakatar da sayar da filaye mallakar jami’ar ba.