✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke barayin jariri mai kwanaki 3 a Kaduna

Kwanaki uku da haihuwar jaririn suka hada baki suka sace shi, cewar mahaifiyar Jaririn mai suna Bilkisu.

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun cafke wasu ma’aurata da kuma wata mata bisa zargin sace jariri mai kwana uku a duniya.

Aminiya ta rawaito yadda aka sace jaririn a ranar 9 ga watan Nuwamba 2020, a Unguwar Mu’azu da ke garin Kaduna.

Mahaifiyar jaririn Bilkisu, ta bayyana a cikin wani bidiyo tana kuka, inda ta kwatanta yadda wata mata ta yaudare ta a yayin da ta je asibiti.

Kakakin ’yan sandan jihar, Muhammad Jagile, a ranar Juma’a ya bayyana cewa a gano jaririn a Jihar Bauchi.

Ya ce wadda ake zargin, ta kulla abotar karya da mai jegon tun kafin haihuwar jaririn.

Kwanaki uku da haihuwar jaririn suka sace shi zuwa wani waje da ba a bayyana ba.

Ya kara da cewa wanda ake zargin an cafke su ne a mobuyarsu, a ranar 26 ga watan Nuwamba 2020, a unguwar Baraya, da ke kan hanyar Jos zuwa Bauchi.

Ya ce an samu jaririn cikin koshin lafiya kuma an damka wa mahaifansa.

Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su, a cewarsa, sannan ya ce za a gurfanar da su gaban kotu domin yanke musu hukunci.

Jami’in ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Umar Muri, ya ja hankalin iyaye da su ke sa ido a kan wanda za suke ba wa ’ya’yansu.