✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke bata-gari 7 da suka kashe mutane a wurin biki a Bauchi

Wadanda ake zargin sun wa jama'a duka a wajen daurin auren.

’Yan sanda sun cafke wasu bata-gari bakwai da suka fantsama a wurin wani daurin aure suka kashe wasu matasa biyu a Gundun Hausawa, Jihar Bauchi.

Mutum biyu da su wadannan bata-garin suka kashe sun hada da mai shekara 17 da kuma mai shekara 18 a duniya.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya shaida wa manema labarai ranar Litinin cewa, “An cafke mutum bakwai da ake zargin na da hannu a faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun shiga inda ake gudanar da bikin ne suka sa duka kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka bude wuta da bindiga, lamarin da ya yi sanadin mutuwar matasan biyu.

Wakil ya ce za su fadada bincike sannan ya roki jama’ar jihar da suke taimaka wa jami’an tsaro da bayanan ayyukan bata-gari a fadin jihar.