✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke dillalan makamai a Katsina

Dillalan sun kware wajen safarar muggan makamai a Katsina da Zamfara.

’Yan sanda a Jihar Katsina sun cafke wasu mutum hudu da suka kware wajen sayar da makamai ga masu aikata laifuka a Jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sanusi Buba ne ya bayyana hakan yayin gabatar wa manema labarai muggan makaman da suka kama, inda ya ce sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne baya samun bayanan sirri.

“Bayanan sirrin da muka samu sun taikama mana wajen kamo wani mutum mai shekar 35 a kauyen Maduru da ke Karamar Hukumar Mani a Katsina.

“Mutumin ya kware wajen safarar makamai ga masu aikata laifi a Katsina da wasu jihohi makwabta.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Katsina, Sunusi Buba yayin da yake nuna makaman da aka masu laifin da su.

“A yayin bincike kuma mun sake gano mutum uku da ke taimaka masa wajen safarar makaman, a kauyukan Sawarya da kuma Maduru.

Daya daga cikin mutanen ya amsa cewar shi ne shugabansu kuma ya dade yana fasakwaurin makamai har zuwa Jamhuriyyar Nijar.

Babbar Bindiga da Harsasai

Sannan ya bayyana cewa ba zai iya tuna adadin makaman da sayar wa masu aikata laifuka ba, amma a cewarsa ya sayar da makamai sama da 10,000.

Mutum biyun da ke taimaka masa kuma sun bayyana wa ’yan sanda cewa su ne suke kai makamai yankunan Gurbi da Dan-Magaji da ke Jihar Zamfara.

Babbar Bindiga Mai Barin Wuta

Kwamishinan ’Yan Sandan ya kara da cewa an samu muggan makamai da suka hada da manyan bindigu, harsasai da tulin kudi da suka kai Naira miliyan 3.4 a hannun wadanda ake zargin.