✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke jami’an Gwamnatin Saudiyya 48 kan rashawa

Jami’an ma’aikatu 6 ciki har da ta tsaro da ta shari’a da wasu baki sun shiga hannu

Gwamnatin Saudiyya ta kame mutane 65 da suka hada da ’yan kasar da wasu ’yan kasashen waje bisa zargin cin hanci da rashawa.

Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Saudiyya (Nazaha) ta ce wadanda ake tuhumar sun hada da jami’an gwamnatin Saudiyya 48 daga ma’aikatun gwamnati guda shida da wasu hukumomi.

M’aikatun sun hada da ta Tsaro, Cikin Cida, Shari’a, Kananan Hukumomi, Karkara da Gidaje, Ilimi, da kuma Muhalli, Ruwa da Noma.

Akwai kuma wasu jami’ai daga Hukumar Tsaron Jiha; da Hukumar Abinci da Magunguna, da kuma Babbar Hukumar Kula da Yanayi da Kare Muhalli.

Tuhume-tuhumen da Nazaha ke musu sun hada da toshiyar baki, amfani da matsayi ba yadda bai dace ba da kuma buga jabun takardu.

An kama jami’an da bakin hauren ne a yayin samamen bincike kusan 460 da hukumar ta Nazha ta yi a watan Fabararirun 2021.

Nahaza ta kama wadanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu mutum 411.

Nazaha ta ce ana kokarin kammala ka’idojin shari’a kafin gurfanar da mutanen a gaban kotu.