✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke Janar din Sojan bogi bayan damfarar N270m

Dan damfarar yana gabatar da kansa a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya

An cafke wani mai mukamin Manjo-Janar din soja na bogi, da ke gabatar da kansa a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya.

Shi dai wannan Manjo-Janar na bogi ya fada komar Hukumar Yaki da Yi Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ne bayan ya yi wa wani kamfani damfarar ta Naira miliyan 270 a Jihar Legas.

Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce an gano bindigogi guda shida da albarusai da sauran kaya da takardun aikin soji na bogi a ofishin Manjo-Janar din na bogi mai suna Bolarinwa Oluwasegun.

“Janar din bogin, Oluwasegun, ya fada hannnun EFCC ne a Legas, bayan an zarge shi da zambar Naira miliyan N270.

“Ya rika gabatar da kansa a matsayin Janar din soja ga kamfanfin Kodef Clearing Resources, wanda ya kawo mana karar shi.

“Oluwasegun ya yaudari kamfanin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana shi da wani mutum domin nadawa a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya.

“Ya shaida wa kamfanin cewa yana bukatar rance na dan lokaci domin ya “bayar da na goro da kuma yin kamun kafa saboda a nada shi a mukamin,” inji Uwujaren.

Jami’in na EFCC ya ce wanda ake zargin ya kuma buga takardar ayyana sunansa, dauke da sa hannun Shugaba Buhari na bogi, wadda ya gabatar wa kamfanin a matsayin shaida domin samun kudaden.

“A wasikar bogin da Oluwasegun ya buga, ya yi ikirarin cewa akwai kudin da zai sanya a Asusun Gwamnatin Tarayya a matsayin daya daga cikin sharuddan nada duk wani Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya.

“Ya buga wasu takardun kuma masu dauke da sa hannun Shugaba Buhari na bogi domin ya samu ya damfari kamfanin, amma dubunsa ta cika a ranar Laraba, 12 ga Janairu, 2022.”

Uwujaren ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar hukumar ta kammala bincike.