✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke ‘likitan’ da ke wa Bello Turji maganin raunin harbi

Ya ce shi ke yi wa Turji magani idan aka harbe shi, yake kuma kai wa ’yan bindiga kayan maye.

Wani jami’in lafiya ya shiga hannu kan yi wa kasurgumin dan bindigan da ya addabi Jihar Sakkwato da Zamfara, Bello Turji, maganin raunin harbi da sojoji suka yi wa dan ta’addar.

Jami’in lafiyan, wanda ke da shagon sayar da magunguna a garin Kamarawa, ya shiga hannu ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai a yankin Gabashin Jihar Sakkwato, inda suka cafke likitan da wasu ’yan bindiga uku a wurare daban-daban.

Ya shaida wa jami’an tsaro cewa shi ne yake yi wa Turji magani idan ya samu raunin harbi a musayar wuta, sannan yana kai wa ’yan bindiga kayan maye.

Da yake bayyana yadda ya hadu da Turji, wanda ake zargin ya ce wani mai suna Musa ne ya hada su kusan shekara uku da suka gabata; “Musa ne ya fara kai ni maboyar Turji a lokacin an harbi Turji a ka, a shekarun baya, na kuma yi masa magani.”

Ya ce ’yan bindiga sukan zo shagonsa sayen kwayoyi da kayan maye ko domin wankin rauni da kuma alluran kashe radadi, amma tun wani lokaci da aka taba kama shi shekara biyu da suka gabata ya tuba.

“A takaice ma na tashi daga can na dawo garin Sakkwato da zama,” inji shi, bayan ya shiga hannu.

A Jihar Katsina kuma, ’yan sanda sun kama wani matashi mai shekara 25, wanda ya ce shi yaron Turji ne.