✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke mai buga jabun kudi a wurin sayen rago

Dubun matashin ta cika ne a yayin da ya je kasuwa sayen rago.

Hukumar Tsaro ta NSCDC ta cafke wani matashi mai shekara 24 bisa zargin damfara da buga jabun kudi a Jihar Nasarawa.

Kwamandan NSCDC, Mamuda Fari, ya ce sun kama matashin ne a kasuwar Shinge da ke Karamar Hukumar Lafia, yayin da yake kokarin sayen rago da jabun kudi.

Ya ce an samu jabun kudi N165,000, a tare da wanda ake zargin wanda ya ce aiki ya yake yi wa wani uban gidansa wanda tuni aka baza komar cafko shi.

Kwamandan ya jinjinawa jami’an sashen yaki da masu damfara na Hukumar kan namijin kokarin da suke yi wajen yaki da laifuka a jihar.

Ya kara da cewa hukumar NSCDC ta fara gudanar da bincike kan lamarin kafin a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.

Sannan ya roki jama’ar jihar da su ci gaba da ba jami’an NSCDC hadin kai da bayanai a duk lokacin da suka ga wani abu da bas u yarda da shi ba.