✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu garkuwa da dailiban Bethel Baptist

An cafke shugabannin gungun masu garkuwar sanye da kayan sojoji.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Makarantar Sakandaren Bethel Baptist da ke Jihar Kaduna sun shiga hannu.

’Yan sanda sun damke uku daga cikin shugabannin gungun ’yan bindigar ne sanye da kayan sojoji, a yayin da daliban makarantar sama da 21 ke hannun masu garkuwar.

A lokacin da kakain Rundunar ’Yan Sanda ta Najeirya, Frank Mba, yake gabatar da su ce a Abuja, dayda daga cikin ’yan bindigar ya ce, “Mu 25 ne muka kai hari makarantar, muka sace dalibai 136 kuma an ba ni N100,000 daga cikin kudin”.

A ranar Lahadi, 19 ga Satumba, 2021, ’yan bindigar suka sako karin mutum 10 daga cikin daliban na Bethel Baptist.

Kawo yanzu akalla mutum 100 daga cikin daliban ne masu garkuwar suka sako bayan sun shafi sama da kwana 80 a hannunsu.

Mafi yawancin daliban na Bethel Baptist da suka dawo wurin iyayensu, an sako su ne bayan iyayensu sun biya kudaden fansa, in banda ’yan kalilan da suka samu suke tsere gda hannun masu garkuwar.