✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu garkuwa da masu fyade 8 a Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta ce za ta sa kafar wando daya da masu aikata migayun laifuka.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kame wasu mutum hudu, bisa zargin yin garkuwa da mutane da wasu huda kuma kan zargin fyade.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Maikudi Shehu ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai.

“Mun samu rahoton yin garkuwa da mutane a yankunan Pindiga, Billiri da Filiya, kuma an karbi kudaden fansa masu yawa.

“Kwanaki biyu da suka gabata wasu masu garkuwa sun shiga har gidan wani mutum suka yi tafi da shi daji, wanda a nan suka tarar da dutse, shi ne suka tsaya hutawa,” cewar Shehu.

Sai dai a cewarsa, mutumin ya tsere daga hannun masu garkuwar, kuma ya sanar da ’yan banga, ’yan sanda da sauran mutanen gari.

Ya kara da cewa, garkuwa da mutane na ci gaba da kamari a Jihar, inda masu mugun aikin suke boye mutane a cikin duwatsu a daji.

“Bayan gano maboyar masu garkuwar, jami’anmu sun bude musu wuta har suka kashe daya daga cikinsu.

“An kame uku daga cikin masu garkuwar, an kuma kashe guda, sai guda uku da suka tsere, kuma nan ba da jimawa ba su ma za a cafke su,” inji Shehu.

Ya ce masu garkuwar an gayyato su ne daga Jihar Adamawa domin su sace wani mutum saboda yana da shanu da yawa.

An cafke masu fyade 4 a Gombe

A wani labarin kuma, Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce jami’an Rundunar sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane, inda masu garkuwar suka tsere suka bar ababen hawansu.

Shehu ya kara da cewa an cafke wasu mutane hudu da suka yi wa yara ’yan shekaru 10 da 14 fyade.

Kwamishinan ya ce laifukan fyade a jihar na ci gaba da karuwa, inda aka samu rahoton aikata laifukan fyade 250, daga ciki an tura 200 zuwa kotu.

Har wa yau, ya ce tun bayan shigowar sabuwar shekara sun samu rahoton laifukan fyade bakwai, amma Rundunar ta su ta fito da hanyoyin maganin hakan, bayan taron masu ruwa da tsaki na jihar da ya gudana.

Sannan ya ba wa al’ummar jihar tabbacin cewa, za su maganin duk wasu bata-gari dake Jihar.

Bayanin gwamnatin Gombe

Kwamishinan tsaron Dauda Zambuk, ya shaida wa manema labarai cewa Gwamnatin Jihar ta shirya maganin masu aikata ta’asa a jihar.

Zambuk, ya ce kwamitin zababbu na jihar, ya  yanke hukuncin samar da ’yan banga na musamman da za su rika taimaka wa ’yan sanda a cikin sassan jihar.

Ya kara da cewa za a dauki mutum 3,080 da za a rabu su mazabu 114 dake jihar.

Sannan kowace mazaba, za a ba ta ’yan banga 25 da za su rika yin sintiri domin rage aikata migayun laifuka.