✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu garkuwa da mutane 11 a Taraba

An gano wadanda ake zargin sun kashe wani jami'in dan sanda a jihar.

Tawagar ’Yan Sanda ta (IRT) ta cafke wasu kasurguman masu garkuwa da mutane 11 a Jihar Taraba.

Mai magana da yawun Rukumar ’Yan Sanda Najeriya, Frank Mba, ne sanae sa hakan, inda ya ce an samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayan tattara wasu bayanan sirri.

A cewarsa, bayanan sun kunshi yadda wadanda ake zargin suke yin garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran manyan laifuka a jihar.

Kazalika, ya ce rundunar IRT ta yi aiki tare da ’yan sandan jihar wajen gano yadda wadanda ake zargin suka sace wani jami’in hukumar Kwastam a jihar da dan uwan Sarkin Jalingo da yadda suka kashe wani dan sanda mai mukamin Sajan a Jihar.

An samu makamai a hannunsu kamar bindiga AK-47, kananan bindigogi, harsashi 121, takunkumin rufe fuska, miyagun kwayoyi da sauransu a yayin da aka kai musu samame.

Ya ce, “Binciken ’yan sanda ya gano suna cikin jerin masu laifin da ake nema ruwa a jallo a jihar Taraba.

“An kuma gano yadda biyu daga cikinsu suka kashe wani jami’in dan sanda tare da raunata wani a yayin da suka sace mutane da dama a baya-bayan nan a Jalingo.”