✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu garkuwa da mutane a Edo

Bayan ware kwanaki bakwai da rundunar soji ta yi a jihar Edo don farautar masu garkuwa da mutane, kwaliyya ta fara biyan kudin sabulu.

Hadin guiwar jami’an tsaro a jihar Edo sun kama wasu mutum bakwai da ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Jami’an tsaron sun kai samame ne a yankin Upper Sakponba na jihar, inda suka yi nasarar kama wadanda ake zargin.

An kama wadanda ake zargin ne a daidai gonar kwakwar manja ta Ogbemundia, kwana daya da sojoji suka fara binciken masu laifuka a jihar.

A satin da ya gabata ne Kwamandan Rundunar ta 2, Manjo Janar Anthony Omozoje ya gana da Gwama Godwin Obaseki kan yadda za a magance ayyukan ’yan ta’adda a jihar.

Ya kuma gana da hukumomin tsaron jihar, inda ya nemi hadin kai wajen kawo zaman lafiya a jihar.

Da yake magana bayan kama wanda ake zargin, Janar Omozoje ya ce rundunarsa na ci gaba da aiki don tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane.

Ayyukan masu garkuwa da mutane da ’yan kungiyar asiri sun addabi Jihar Edo, har ta kai ga gwamnan jihar ya gana da masu ruwa da tsaki domin magance matsalar tsaro da take barazana ga zaman lafiyar jihar.