✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke masu kwacen babur 2 a Neja

Jama'ar gari sun yi wa masu kwacen babur din tara-tara sannan suka kama su.

Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da kwacen babura, a Minna babban birnin Jihar.

Wanda ake zargin su biyu sun shiga hannun jam’an tsaro ne da misalin karfe 2:30 na yamamcin ranar Lahadi, yayin da suka yi kokarin kashe wani mutum tare da kwace masa babur.

Masu kwacen, sun taso daga unguwar Fadukpe da ke Minna zuwa yankin Shanu, inda suka doke wani mutum mai suna Mohammed Idris Sakewa a ka, sannan suka yi yunkurin kwace babur din daga hannunsa.

Wani shaidar gani da ido, ya ce mutumin da suka yi kokarin kwace wa babur ya kurma ihu don jan hankalin jama’a.

Kazalika, ya ce nan take jama’ar yankin suka farmaki barayin sannan suka kama su tare da mika su ga ’yan bangar yankin Fadikpe, wanda su kuma suka mika su ga jami’an na ’yan sanda.

Tuni dai aka garzaya da mutumin zuwa asibitin Unguwan-Daji da ke Minna don ba shi kulawa.