✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu manyan laifi 297 a Kano

Za a gurfanar da ababen zargin a gaban Kuliya da zarar an kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Kano ta yi nasarar cafke gungun masu aikata miyagun laifuka 297 a fadin Jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan da cewa an cafke ababen zargin a wurare daban-daban a fadin jihar.

Ya ce, matakin hakan na zuwa ne a wani yunkuri na dakile yawaitar faruwar miyagun laifuka da rundunar ’yan sandan ta sanya a gaba.

“An yi kamen masu laifun ne daga 10 ga Afrilu zuwa 23 ga Mayu, musamman gabani da kuma bayan bikin karamar sallah,” a cewar Kiyawa.

Ya shaida cewa, sun bankado maboyar wadanda ake zargi da aikata laifukan da suka hada da garkuwa, fizge da kuma fadan daba.

Kakakin ya ce daga cikin wadanda aka cafke, mutum 187 ana zarginsu da laifin fadan daba, sai mutum daya da yake damfarar mutane da katin banki na ATM da kuma mutum daya da laifin safarar mutane.

Ya ce wasu mutum 80 kuma ana zarginsu da laifin damfara da fashi da makami, biyar kuma da laifin safarar miyagun kwayoyi da kuma mutum bakwai masu kwacen wayoyin mutane.

Kazalika, ya ce jami’ansu sun yi nasarar cafke wasu manyan masu garkuwa da mutane bakwai da kuma mutum bakwai masu satar mota.

Kazalika, ya ce rundunar ta kwato makamai masu hadari kamar bindigar hannu da alburusai masu tarin yawa.

Daga cikin ragowar abubuwan da aka kwato sun hada da Babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu, wayoyin hannu, miyagun kwayoyi da sauransu.

Kiyawa, ya ce rundunar za ta gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kuliya da zarar sun kammala binciken da suke gudanarwa a kansu.