✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu satar mutane daga tashar mota a Kano

Jagoran gungun na shiga cikin fasinjoji ko ya dauke su a bas din haya.

’Yan sanda sun cafke gungun wasu masu satar mutane da ke zuwa tashoshin mota a matsayin fasinja ko direba suna kafa wa matafiya tarko domin yin garkuwa da su.

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce dubun masu satar mutanen ta cika ne bayan ’yan sanda sun gano shirinsu na sace matafiya a kan titin Kano zuwa Katsina.

Ta kara da cewa jami’an rundunar sun yi nasarar kwato gurneti 11 da bindigogi 11 da motoci 15 a hannun gungu-gungu na mutanen da ake zargi da aikata miyagun laifuka.

Sanarwar da kakakin rundunar, Frank Mba, ya fitar ta ce, wani matashi mai shekara 25 ne ke jagorantar gungun mutum tara masu sace matafiyan, kuma dukkansu shekarunsu 22 ne zuwa 30, sai mutum daya mai sheka 45.

Ya ce jagoran gungun, mai suna Bashir Sule ne ke yin sojan gona a matsayin direban bas din haya, inda yake zuwa tasha ya lodin fasinjoji ya bi da su ta wurin da suka tsara da abokansa.

Idan an je kan hanya sai yaran nasa su fito daga cikin daji su far wa matafiyan su yi musu fashi su yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa.

A wani lokaci kuma shugaban gungun kan shiga bas din haya a matsayin fasinja, inda yake ba wa yaransa bayanai motar da ya shiga, su kuma sai su jira isowarta, su tare ta, su sace mutanen cikinta, ba tare da komai ya same shi ba.

  1. An kama mata masu garkuwa

Rundunar ’yan sandan ta ce jami’anta sun kuma cika hannu da wasu mutum 11 – ciki har da mata biyu – da suka yi kaurin suna wajen yin fashi da garkuwa da mutane, gami da fasakwaurin makamai.

Sanawar ta ce matan da ke cikin gungun ne suke yi musu safarar makamansu kafin daga baya dubunsu ta cika.

Ta ce ta kama masu satar motoci da Najeriya suna fasakwaurinsu zuwa Jamhuriyar Nijar, ta kuma kwato motoci 15 daga hannununsu.