✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu tallan maganin gargajiya 13 a Kano

Hukumar da ke sa ido kan cibiyoyin kula da lafiya masu zaman kansu a jihar Kano (PHIMA), ta cafke masu tallan maganin gargajiya 13 sakamakon…

Hukumar da ke sa ido kan cibiyoyin kula da lafiya masu zaman kansu a jihar Kano (PHIMA), ta cafke masu tallan maganin gargajiya 13 sakamakon amfani da kalmomin batsa yayin da tallata hajarsu ta magungunan gargajiya a birnin Kanon Dabo.

Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar, Abba Dalha Soron Dinki ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar.

An dai yi nasarar kame masu maganin gargajiyar a cibiyar Alfurqan da unguwar Fagge da Sharada da kuma Masallacin Juma’a na Ja’en.

Sauran wuraren da aka kama masu maganin sun hada da babban hanyar Sabon titi da yankin Gurin Gawa da Titin gidan Zoo.

Soron Dinki ya bayyana cewa, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano tana kokarin tsaftace tallace-tallacen magungunan gargajiya barkatai da masu amfani da kalaman batsa yayin da suke neman masu saye.

Ya ce gwamnatin Kano ta shirya tsaf domin kawo tsafta cikin duk wata harka da ta shafi kiwon lafiya, wanda shi ne dalilin da yasa gwamnatin kafa kwamiti domin yaki da masu aikata irin wannan laifi.

Kamun masu amfani da kalaman batsa yayin tallan maganin gargajiya, na zuwa ne makonni biyu da gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai shiga sa kafar wando daya da duk wanda aka kama da irin wannan laifi.

An kafa Kwamitin ne a karkashin jagorancin Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa, sai hukumar Hisbah, Karota da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar lafiya a matsayin mambobinta.

Wannan matsala ta amfani da kalaman batsa wajen tallan magungunan gargajiya a Arewanci Najeriya, ta dade tana ciwa mutane tuwo a kwarya.

A Kano, kafin zuwan Gwamna Abdullahi Ganduje, sai da tsohuwar gwamnatin jihar karkashin Dokta Rabi’u Kwankwaso ta shiga yaki da masu irin wannan dabi’a ta amfani da kalaman batsa yayin tallan magungunan gargajiya.