✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu yi wa ’yan fashi safarar makamai a Kaduna

Sun yi nufin kai wa ubangidansu makaman ne don fashi da makami a Kaduna.

Wata Kotun Majistare a Kaduna ta tsare wasu mutum biyu a gidan yari bisa zargin mallakar bindigogi ta haramtacciyar hanya.

Yayin zaman kotun a ranar Laraba, Alkali Ibrahim Emmanuel, ya ba ba umarnin a tsare wadanda ake zargin kafin kotun ta samu shawara daga Darakatan sashen tuhuma na jihar.

Da farko dan sanda mai tuhuma, Sufeto Sunday Baba, ya shaida wa kotun an cafke wadanda ake zargin ne a watan Disamba a unguwar Rigasa suna dauke da bindigogi kirar gida da adduna da wukake.

Ya ce sun yi ikirarin za su kai makaman ne ga ubangidansu a matsayin kayan aikin fashi da makami.

Ya kara da cewa, har yanzu ’yan sanda suna farautar ubangidan nasu wanda ya yi layar zana.

Kotun ta ki karbar rokon wadanda ake tuhumar, sannan Alkalin ya dage shairi’ar zuwa 6 ga Fabrairu.

(NAN)