✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke matashi kan sukar Gwamnan Yobe a kafafen sada zumunta

Za a gurfanar da yaron a kotu da zarar 'yan sanda sun kammala bincike.

Wani matashi mai shekara 16 ya shiga hannun hukuma bayan an zarge shi da cin zarafin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a kafafen sada zumunta.

Jami’an tsaro sun cafke matashin tun a ranar 11 ga watan Disamba, 2022 amma labarin bai bayyana ba sai a ranar Litinin lokacin da mahaifin yaron ya bukaci a sakar masa da.

Rahotanni sun ce an cafke matashin ne a garin Nguru, wanda daga bisani kuma aka dauke shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sanda Jihar da ke Damaturu.

Mahaifin yaron mai suna Garba Haruna, wanda ke sana’ar wanki da guga, ya roki Gwamnan Jihar da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar da su saki dansa.

“Na yi nadamar abin da dana (Umar) ya aikata. Ni ba kowa ba ne face mai wanki da guga, ina rokon Gwamna Mai Mala Buni da ’yan sanda da su taimaka su yafe masa kuma su sake shi,” inji mahaifin yaron.

Da aka tuntubi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, ya ce yaron yana tsare kuma da zarar sun kammala bincike za su mika shi zuwa kotu.

“Da zarar mun kammala bincike za a mika shi kotu. Mutane suna amfani da kafafen sada zumunta wajen bata sunan mutane, don haka akwai bukatar kawo gyara a cikin al’umma.

“Ba zai yiwu mutane su rika wallafa duk abin da suka ga dama ba. Akwai doka da oda a Najeriya. Duk wanda aka samu da laifi dole ne ya fuskanci hukunci,” cewar Kwamishinan.