✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke matsafa da sassan jikin mutum sabon yanka

’Yan sanda sun kamo bayan sun yi kokarin tsere wa hukuma.

Wasu matsafa biyu sun shiga hannu a lokacin da suke dauke da sassan jikin mutum sabon yanka za su kai wa boka a Jihar Kwara.

Dubun matsafan ta cika ne a kusa da wani shingen binciken ababan hawa a kan hanyar Oke Oyi zuwa Jebba na jihar ranar Lahadi, inda da ganin ’yan sanda wadanda ake zargin suka ranta a na kare a kan babur dinsu.

“Halin da suka nuna ya sanya wa ’yan sandan da ke wurin binciken shakku, nan take ’yan sandan suka bi su suka kamo su.

“An gano kan mutum da wasu sassan jiki a cikin jakar da aka kama su dauke da ita,” a cewar Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, ASP Ajayi Okasanmi.

Ya kara da cewa, mutum biyun da aka cafke din sun fito ne daga Share cikin Karamar Hukumar Ifelodun ta jihar, kuma sun tabbatar cewa za su kai sassan jikin ne wurin wani boka a Ilorin don tsafi.

Daga nan, ya gargadi matsafa da sauran masu aikata manyan laifuka a jihar da su shiga taitayinsu ko su fice daga jihar saboda a cewarsa hukuma ba za ta raga musu ba.