✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke mutum 2 da AK47 da alburusai 325 a Zamfara

Ana zargin mutum biyun da safarar makamai daga Jihar Benuwe.

Wasu mutum biyu dauke da bindiga kirar AK47 da albarusai 325 sun shiga hannu a kan hanyar Gusau-Wanke-Dansadau a Jihar Zamfara.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Mohammed Shehu ne, ya ce mutanen, mace da na miji, sun shiga hannu ne a wani shingen bincike da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu.

Ana zargin su da sayar da bindigogi da dama a dazukan Zamfara da jihohin da ke makwabtaka da su.

Shehu, ya ce an cafke mutanen ne bayan bayanan sirri da rundunar ta samu kan safarar makamai da Benuwai zuwa sansanin ’yan bindiga a Zamfara.

Ya ce za a ci gaba da bincike domin cafke wadanda ake zargin tare suke gudanar da muguwar sana’ar tasu don gurfanar da su a gaban kotu.

Kazalika, Shehu ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Kolo Yusuf, ya ba da tabbacin  rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.