✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke mutum 43 bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi a Kano

Shugaban hukumar reshen jihar Kano, ya yaba da nada Buba Marwa, a matsayin shugabanta.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Kano ta ce ta kame mutane 43 bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.

Hakan ya fito ne daga bakin shugaban hukumar na jihar, Dakta Ibrahim Abdul, yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Juma’a.

A cewarsu, “A iya watan Janairu, bayan sumame da mu kai kai a wurare da dama, mun kama kayan maye da nauyinsu ya kai kilo 581.702.

“Tsawon lokacin an kamo mutum 76 da ke bukatar gyaran hali, sai mutum hudu da aka killace, sannan aka sallami mutum biyu,” cewar Abdul.

Shugaban hukumar ya kara da cewa masu laifin an kama su ne a wurare daban-daban dake cikin jihar.

Bugu da kari, ya ce nasarar da hukumar ke samu ta samo asali ne da irin kokari da jami’an hukumar da masu ruwa da tsaki ke yi a jihar wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.

Daga nan sai ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda nada Buba Marwa a matsayin sabon shugaban hukumar ta NDLEA.