✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke mutumin da ake zargi da kashe Jamal Khashoggi

Ana zargin wasu makusantan yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman da hannu a kisan Khashoggi.

Wani mutum dan kasar Saudiyya da ake zargi da hannu a kisan dan jarida Jamal Kashoggi ya shiga hannu a birnin Paris na Kasar Faransa a ranar Talata.

Mutumin mai shekara 33 an tsare shi ne a filin jirgi da misalin karfe 9:30 na safe, kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana.

Mutumin mai suna Khaled Aesh Al-Otaibi, radiyon RTL ta ce ba a bayyana wa manema labarai dalilin cafke shi ba.

Khashoggi, dan jarida ne dan kasar Saudiyya wanda ake zargin yana takun saka da yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman.

An kashe shi tare da yi wa sassan jikinsa gunduwa-gudunwa ne a ranar 2 ga watan Oktoban 2018 a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya.

Ana zargin wasu makusantan Yarima Mohammed Salman da kashe dan jaridar.

Al-Otaibi na daya daga cikin mutum 16 da kasar Amurka ta hana shiga kasarta tun a watan Afrilun 2019, kan zargin su da hannu a kisan Jamal Khashoggi.