✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke shi da katin ATM 5,000 a hanyar Dubai

An kama katunan ne a cikin buhun wake a lokacin da mutumin ke kokarin hawa jirgi daga Kano zuwa Dubai

An kama wani mutum yana kokarin fita kasar waje da katin cirar kudi guda 5,342 a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa ta ce ta kama wanda ya boye katunan a cikin buhun wake ne zai haw jirgi zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kwanturolan hukumar mai kula da shiyyar Kano da Jigawa, Nasir Ahmed, ya ce “akwai alamar tambaya; Mun tabbata akwai wadanda suke hada baki da shi.

“Takardarsa ta izinin zama a Dubai ta nuna ya jima yana yin irin wannan harka.

“Za mu bincika mu gano sau nawa ya yi hakan daga Najeriya domin a hada laifukan a gurfanar da shi a gaban kotu”.

Jami’in ya ce an mika mutumin ga hukumar EFCC tare da bayar tabbacin cewa za ta gano masu katunan da aka kama da kuma dalilin mutumin na daukar katunan zuwa Dubai.

“Za ta sanar da mu abin da ta gano kuma da zarar an samu hujjoji a kan wanda ake zargin da mukarrabansa za a gurfanar da su a kotu”, inji shi.