✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke wani da bindigogi 8 a tashar mota a Abuja

Mutumin ya ba da sakon bindigogi kira AK-47 a kai mishi su Kano daga Abuja

An cafke wani mutum dauke da bindigogi takwas ya shiga hannu a tashar motar Zuba da ke Abuja.

’Yan banga ne dai suka cafke mutumin a ranar Laraba a lokacin da yake kokarin ba sakon bindigogin domin a kai mishi su zuwa Jihar Kano.

Kwamandan ’yan bangar yankin Zuba, Yahaya Madaki, ya ce sun mutumin ta cika ne bayan ya je tashar ya nemi a hada shi da direban da ke lodi zai ba da sakon makaman a kai masa su Kano.

“Sai aka nuna mishi direba da ke lodi a lokacin sai ya ba direban kayan a cikin kwali da lambar wayar wanda zai karbi Kayan a Kano.

“Aka ce masa kudin kayansa N10,000 wanda nan take ya biya.

“Sai direban ya nemi tabbatar da kayan da ke cikin kwalin amma mutumin ya ki, sai ya yi kokarin tserewa amma jama’a suka rutsa shi,” in ji Madaki.

Ya ce da ka bincika sai aka samu bindigo biyar kirar AK-47 da wasu kirari Pump Action a cikin kwalin.

Rahotanni sun bayyana cewa DPO na yankin Zuba, CSP Osor Moses, da kansa ya jagoranci tarar mutumin.

Sai dai da wakilanmu ya runtube shi DPO bai yi magana ba, amma ya ce a sami Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Abuja, DSP Josephine Adeh, wadda ita kuma ta ce za ta bincika ta yi mana karin haske.

Sai dai kuma har muka kammala hada wannan rahoto ba mu ji daga gare ta ba.