✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke ‘yan Kano masu sayar da hotunan mata na batsa

Wasu mutanen Jihar Kano sun shiga hannun rundunar ’yan sanda saboda zarginsu da aikata laifin cin zarafin mata ta hanyar lalata da yadawa a manhajar…

Wasu mutanen Jihar Kano sun shiga hannun rundunar ’yan sanda saboda zarginsu da aikata laifin cin zarafin mata ta hanyar lalata da yadawa a manhajar WhatsApp.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Frank Mba yayin zantawarsa da BBC.

Mista Frank ya ce jami’an ’yan sandan kasa da kasa na Interpol a Abuja ne suka cafke mutanen da ke cin kasuwa ta hanyar yada bidiyo da hotunan batsa na mata a shafin manhajar WhatsApp mallakin wani dan Kasar Brazil.

Ya ce an samu nasarar cafke mutanen ne sakamakon tattara bayanan sirri ta hanyar hadin gwiwa da jami’an Interpol a Brazil.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka samu a hannun ababen zargin sun hada da wayoyin salula uku da kwamfutar tafi da gidanka ta Laptop.

Kazalika, rundunar ’yan sandan ta ce ta samu bidiyo da daman na ’yan mata ’yan kasa da shekara 18 da aka sayar a yanar gizo.

Baya ga haka, rundunar ta ce ta samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargi da garkuwa da mata da kananan yara a jihohin Kudu maso Kudancin Najeriya sannan tana tsare da mutum biyar masu garkuwa da mata da kananan yara a Jihar Fatakwal.

Wata sanarwa da Sufeton ’Yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya fitar ta ce, shirin rundunar da aka tanada domin dakile cin zarafin mata da kananan yara a Najeriya ya fara haifar da da mai ido.

A yayin da rundunar ’yan sandan ke ci gaba da tsananta bincike domin bankado miyagu, ta ce ta samu nasarar cafke jimillar mutum 2,792 da ake zargi da aikata laifuka masu nasaba da cin zarafin mata a bara.

Babban Sufeton ’yan sandan kasa ya gargadi iyaye da su rika lura da tarbiyar ’ya’yansu da duk wani shige da ficensu tare da bayar da rahoton duk wani nau’i na cin zarfi da aka yi wa mata da kananan yara ba tare da jinkiri ba.