✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceci dattijon da aka daure shekara 30 a Kano

Dangin mutumin mai shekaru 55 sun yi masa daurin talala a jikin wani gungume a wani kuntataccen daki

Wani dattijo da aka daure na shekara 30 saboda tabin hankalin da ke damunsa ya samu kubuta da taimakon ‘yan sanda a garin Rano a Jihar Kano.

‘Yan uwan dattijon mai shekara 55 da ba kai ga tantance sunansa ba sun daure shi ne a jikin wani gungume da aka yi wa marikan karfe.

A cewar ‘yan sandan, mutumin ya shafe tsawon shekarun ne daure a jikin wani gungume cikin wani kuntataccen daki da ko taga babu.

Da ya ke tabbatar da hakan, Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an garzaya da mutumin zuwa wani asibiti dake Karamar Hukumar Rogo domin ya ci gaba da samun kulawa.

Ya kuma ce sun fara bincike a kan lamarin don gano hakikanin dalilin daure shi.

A makancin labarin da BBC ta ruwaito, wani mai fafutikar kare hakkin dan Adam, Sani Shuaibu ya ce” “Mutumin yana da tabin hankali kuma ya fara fada. Maimakon a nemo masa magani tun a 1990, sai mahaifinsa ya yanke shawarar daure shi” .

Bayan rasuwar mahaifinsa a shekarun baya, sai ‘yan uwan mutumin mai shekaru 55 suka ci gaba da kulle shi.

Ya ce bayan ya samu labarin halin da mutumin ke ciki, sai ya sanar da ‘yan sanda, wadanda suka ceto shi tare da taimakon wasu makwabta.

Shu’aibu ya kuma ce an garzaya da mutumin Babban Asibitin garin Rano, inda yanzu yake karbar magani.

Wannan dai shi ne karo na uku da ake ceto mutane daga kullen da danginsu ke yi musu cikin kasa da mako daya a jihar.

Ko a cikin makon nan dai ‘yan sandan sai da su ka ceto wani wanda aka daure shekaru bakwai da wanda aka daure shekaru 15 ba tare da samun cikakkiyar kulawar lafiya ba.

Gabaninsa an ceto wani wanda iyayensa suka kulle a daki na shekara bakwai a daki saboda zarginsa da shan miyagun kwayoyi.