✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceoto mutum 77 daga masu garkuwa a Katsina

Ranar Juma'a za a mika mutanen da aka kubutar a Batsari da Jibia ga iyalansu

Jami’an tsaro sun kubutar da mutum 77 daga hannun masu gakuwa da mutane a Jihar Katsina suka kuma mika su ga Gwamna Aminu Masari.

Gwamnan ya ce an kubutar da mutanen ne da hadin gwiwar kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), ’yan sanda, sojoji, hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro.

“Mun samu dama kuma muna aiki tare da shugabannin Miyetti Allah tare da ’yan sanda, sojoji, DSS, sojin sama da sauran hukuomin tsaro domin dawo da duk abin da za mu iya na mutanen da aka yi garkuwa da su”, inji shi.

Aminiya ta gano cewa a ranar Juma’a aka sa ran sada mutanen su 77 da aka kubutar a yankin Jibia da Batsari da iyalansu.

Masari ya ce irin wannan hadin gwiwar ta ba da damar kubutar da mutum 104 da aka yi garkuwa da su bayan-bayan nan.

Ya ce daga cikinsu, 16 an kubutar da su ne a yankin Sabuwa, Faskari da Dandume na Jihar; 10 kuma a yankin Danmusa; sai kuma mutum 77 da aka hannanta a ranar Alhamis a yankin Batsari da Jibia.

Gwamnan Jihar ta Katsina ya kara da cewa hadin gwiwar kari ne a kan tattaunawar da ta kai ga kubutar da dalibai 344 da ’yan bindiga suka sace daga Makanatar Kankara.

“An ci gaba da tattaunawa, kuma ana yi ne cikin sirri domin kada a jefa rayuwar kowa a cikin hadari da kuma nufin kawo karshen ayyukan garkuwa da mutane,” inji shi.

Kwamishinn ’Yan Sandan Jihar Katsina, Sanusi Buba, a jawabinsa, ya ce su kansu ’yan binidgar sun sha neman a samu zaman lafiya a yankunansu.

Ya ce, “An jima ana wannan aiki. Muna kokarin ganin an sako duk mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da an biya kudin fansa ko an cutar da su ba.

“Muna fatar wannan hanya ba za ta takaita ga Jihar Katsina kadai ba, za ta kai ga zuwa jihohin da ke fuskantar wannan barazana.”