✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto dalibai 200 bayan harin GSSS Kankara

Hukumomi na ci gaba da kirge domin tabbatar da yawan wadanda suka bace

An gano dalibai kimanin 200 da suka tsere bayan ’yan bindiga sun kai hari a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) da ke Kankara, Jihar Katsina.

Daliban da harin na tsakar dare ya sa suka arce zuwa cikin daji sun dawo cikin koshin lafiya kamar yadda hukumar makarantar da ’yan sanda suka tabbatar.

Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, Gambo Isah da Shugaban Makarantar, Usman Abubakar ne suka tabbatar da haka ranar Asabar bayan rahotanni sun nuna daruruwan dalibai sun bace bayan harin da aka kai ranar Juma’a da tsakar dare.

Malam Usman ya ce hukumar makarantar na kan kirga daliban domin tabbatar da hakikanin halin da ake ciki game da wadanda suka bace ko aka yi garkuwa da su.

“Ba za mu iya sanin yawan daliban da aka yi garkuwa da su ba sai daga baya saboda wasu daliban da ba a gani ba da farko na ta dawowa daga cikin daji; Yanzu dai muna kiran rajista ne.

“Wasu daliban kuma gida suka koma, iyayensu ne suka kira suka shaida wa hukumar makaranta”, inji shugaban makarantar.

A nasa bangaren, kakakin ’yan sandan jihar, ya ce mahara dauke da manyan bindigogi sun far wa GSSS Kankara ne da misalin 11:30 na dare.

“Jami’anmu sun yi musayar wuta da su, wanda hakan ya sa dalibai suka samu suka tsere.

“Da safen nan DPO ya gano sama da 200 daga cikin daliban ya kuma mayar da su makaranta.

“Muna ci gaba da kirge domin tabbatar da ko maharan sun yi garkuwa da wani dalibi.

“Da ma can an riga an girke ’yan sanda suna gadin makarantar, su ne suka yi musayar wuta da ’yan bindigar.

“Maharan sun harbi jami’inmu kuma an garzaya da shi asibiti inda ake jinyarsa”, inji shi.

A daren Asabar ne ’yan bindiga dauke da manyan makamai suka yi wa makarantar dirar mikiya a harin da suka kai na kusan awa guda.