✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto jaririn da aka sayar mako daya da haihuwarsa

Gwamnatin Jihar Edo ta ceto wani jariri dan kimanin sati daya da haihuwa daga hannun masu cinikin jarirai a tsakanin jihar da kuma Anambra. Kwamishinar…

Gwamnatin Jihar Edo ta ceto wani jariri dan kimanin sati daya da haihuwa daga hannun masu cinikin jarirai a tsakanin jihar da kuma Anambra.

Kwamishinar Shari’a ta Jihar kuma shugabar kwamitin yaki da safarar mutane a Jihar, Farfesa Yinka Omorogbe ta ce dillalan sun sayar da jaririn a kan N300,000, kuma an gurfanar da su a kotu domin su girbi abun da suka shuka.

“A ranar 5 ga Agusta, sashen bincike na kwamitinmu ya gano wani gidan da ake amfani da shi wajen cinikin jarirai a jihohin Edo, Anambra da wasu sassan kasar nan.

“Bayan mun kama daya daga cikin dillalan mun titsiye ta, sai ta fada mana sunan wata mata a Jihar Anambra, inda a nan ne gidan cinikin jariran yake”, inji ta.

Ta kuma ce bayan da suka kama matar ta Anambra sai ta shaida wa jami’ansu cewa jaririn da mahaifiyarsa na zaune ne a wani asibiti.

Daga bisani matar ta jagoranci ‘yan kwamitin zuwa asibitin da matar ta haifi jaririn tare da kama unguwarzomar da ke karbar haihuwa a wurin.

Ta ce kwamitin ya gano wata budurwa da ta haihu ranar 28 ga watan Yuli da aka sayar da jaririn nata bisa alkawarin za a ba ta Naira 300,000 a matsayin kasonta.

“Mun kuma samu matar da wata budurwar wacce ke dauke da juna biyu kuma ta kusa haihuwa kuma ta kasa cikakken bayanin makasudin zamanta a gidan”, inji shugabar kwamitin.